Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
25 verses
1Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.
2Ubangiji ya ce,“Kada ku koyi abubuwan daal'ummai suke yi,Kada ku ji tsoron alamun da suke asama,Ko da yake al'ummai suna jintsoronsu.
3Gama al'adun mutane na ƙarya ne,Daga cikin jeji aka sare wani itace,Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi dagizago.
4Mutane sukan yi masa ado na azurfada zinariya,Sukan ɗauki guduma su kafa shi daƙusoshi,Don kada ya motsa.
5Gumakansu dodon gona suke, acikin gonar kabewa,Ba su iya yin magana,Ɗaukarsu ake yi domin ba su iyatafiya!Kada ku ji tsoronsu.Gama ba su da ikon aikata muguntako alheri.”
6Ya Ubangiji, ba wani kamarka,Kai mai girma ne,Sunanka kuma yana da girma daiko.
7Wane ne ba zai ji tsoronka ba, yaSarkin dukan al'ummai?Ka isa a ji tsoronka,Gama babu kamarka a cikin dukanmasu hikima na al'ummai,Da kuma cikin dukan mulkokinsu,Ba wani kamarka.
8Dukansu dakikai ne wawaye,Koyarwar gumaka ba wani abu bane, itace ne kawai!
9An kawo fallayen azurfa dagaTarshish,Da zinariya kuma daga Ufaz,Aikin gwanaye da maƙeranzinariya.Tufafinsu na mulufi ne da shunayya,duka aikin gwanaye.
10Amma Ubangiji shi ne Allah nagaskiya,Shi Allah mai rai ne,Shi Sarki ne madawwami.Saboda hasalarsa duniya ta girgiza,Al'ummai ba za su iya jurewa dafushinsa ba.
11Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”
12Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya,Ta wurin hikimarsa ya kafa ta,Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗasammai.
13Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙuginruwa a cikin sammaiYakan kawo ƙasashi daga ƙurewarduniya,Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwansama,Daga cikin taskokinsa yakan kawoiska.
14Kowane mutum dakiki ne, mararilimi,Kowane maƙerin zinariya zai shakunya saboda gumakansa,Gama siffofinsa ƙarya ne,Ba numfashi a cikinsu.
15Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne,A lokacin da za a hukunta su za sulalace.
16Gama shi ba kamar waɗannan yakeba,Shi na Yakubu ne.Shi ne ya yi dukan kome,Kabilan Isra'ilawa gādonsa,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.
17Ku tattara kayayyakinku,Ku mazaunan wurin da aka kewayeda yaƙi.
18Gama haka Ubangiji ya ce,“Ga shi, ina jefar da mazaunanƙasar daga ƙasarsu a wannanlokaci,Zan kawo musu wahala, za su kuwaji jiki.”
19Tawa ta ƙare, saboda raunin da akayi mini.Raunina mai tsanani ne,Amma na ce, lalle wannan azaba ce,Tilas in daure da ita.
20An lalatar da alfarwata,Dukan igiyoyi sun tsintsinke,'Ya'yana maza sun bar ni, ba sunan.Ba wanda zai kafa mini alfarwataYa kuma rataya labulena.
21Makiyayan dakikai ne,Ba su roƙi Ubangiji ba,Don haka ba su sami wadata ba,An watsa dukan garkensu.
22Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shikuma, yana tafe.Akwai babban hargitsin da ya fitodaga arewa,Don a mai da biranen Yahuza kufai,wurin zaman diloli.
23“Ya Ubangiji, na sani al'amuranmutum ba a hannunsa suke ba,Ba mutum ne yake kiyaye takawarsaba
24Ka tsauta mini, ya Ubangiji, ammada adalcinka,Ba da fushinka ba, don kada kawofinta ni.
25Ka kwarara hasalarka a kan sauranal'umma da ba su san ka ba,Da a kan jama'ar da ba su kiransunanka,Gama sun cinye Yakubu,Sun cinye shi, sun haɗiye shi,Sun kuma mai da wurin zamansakufai.”