Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
26 verses
1Da ma kaina ruwa ne kundum,Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne,Da sai in yi ta kuka dare da rana,Saboda an kashe jama'ata!
2Da ma ina da wurin da zan fake ahamada,Da sai in rabu da mutanena, in tafican!Gama dukansu mazinata ne,Ƙungiyar mutane maciya amana.
3Ubangiji ya ce,“Sun tanƙwasa harshensu kamarbaka,Ƙarya ce take rinjayar gaskiya aƙasar.Suna ta cin gaba da aikata mugunta,Ba su kuwa san ni ba.
4“Bari kowane mutum ya yi hankalida maƙwabcinsa,Kada kuma ya amince da kowaneirin ɗan'uwa,Gama kowane ɗan'uwa munafukine,Kowane maƙwabci kuma mai kushene.
5Kowane mutum yana ruɗinmaƙwabcinsa da abokinsa,Ba mai faɗar gaskiya,Sun koya wa harshensu faɗarƙarya.Suna aikata laifi,Sun rafke, sun kasa tuba.
6Suna ƙara zalunci a kan zalunci,Yaudara a kan yaudara,Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.
7Saboda haka, Ubangiji MaiRunduna, ya faɗa cewa,“Zan tsabtace su, in gwada su,Gama me zan yi kuma sabodajama'ata?
8Harshensu kibiya ce mai dafi, yanafaɗar ƙarya,Kowa yana maganar alheri damaƙwabcinsaAmma a zuciyarsa yana shirya masamaƙarƙashiya.
9Ba zan hukunta su saboda waɗannanal'amura ba?Ba zan sāka wa al'umma irinwannan ba?”
10Zan yi kuka in yi kururuwa sabodatsaunuka,Zan yi kuka saboda wuraren kiwo,Domin sun bushe sun zama marasaamfani.Ba wanda yake bi ta cikinsu.Ba a kuma jin kukan shanu,Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudusun tafi.
11“Ni Ubangiji na ce, zan mai daUrushalima tsibin kufai,Wurin zaman diloli,Zan kuma mai da biranen Yahuzakufai, inda ba kowa.”
12Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?
13Sai Ubangiji ya ce, “Saboda sun bar dokata wadda na sa a gabansu, ba su yi biyayya da maganata ko su yi aiki da ita ba.
14Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.
15Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.
16Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.
17“Haka ni Ubangiji Mai Runduna nace,Ku yi tunani, ku kirawo mata masumakoki su zo,Ku aika wa gwanaye fa.”
18Jama'a suka ce,“Su gaggauta, su ta da murya,Su yi mana kuka da ƙarfi,Har idanunmu su cika da hawaye,Giranmu kuma su jiƙe sharaf.
19“Gama ana jin muryar kuka dagaSihiyona cewa,‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatarda mu ɗungum!Don mun bar ƙasar, domin sunrurrushe wuraren zamanmu.’ ”
20Irmiya ya ce,“Ya ku mata, ku ji maganarUbangiji,Ku kasa kunne ga maganar da yafaɗa,Ku koya wa 'ya'yanku mata kukanmakoki,Kowacce ta koya wa maƙwabciyartawaƙar makoki,
21Gama mutuwa ta shiga tagoginmu,Ta shiga cikin fādodinmu,Ta karkashe yara a tituna,Ta kuma karkashe samari a dandali.
22Ubangiji ya ce mini,‘Ka yi magana, cewa gawawwakinmutane za su fāɗi tuliKamar juji a saura,Kamar dammunan da masu girbisuka ɗaura,Ba wanda zai tattara su.’ ”
23Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.
24Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”
25Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa'ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya,
26da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”