Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
22 verses
1“Ni Ubangiji na faɗa, cewa a wancan lokaci, za a fitar da ƙasusuwa daga kaburburan sarakunan Yahuza, da na sarakansu, da na firistoci, da na annabawa, da na mazaunan Urushalima.
2Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.
3Sauran mutanen muguwar tsaran nan waɗanda suke a wuraren da na warwatsa su, za su fi son mutuwa fiye da rayuwa. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
4“Ka faɗa musu, ka ce, ni Ubangiji nace,‘Wanda ya fāɗi ba zai sāke tashi ba?Idan wani ya kauce ba zai komo kanhanya ba?
5Me ya sa, mutanen nan naUrushalima suke ratsewa, sukekomawa baya kullayaumin?Sun riƙe ƙarya kan-kanSun ƙi komowa.
6Na kula sosai, na saurara,Amma ba wanda ya faɗi watamaganar kirki,Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa,Kowa cewa yake, “Me na yi?”Kamar dokin da ya kutsa kai cikinfagen fama.
7Ko shamuwa ta sararin sama ma, tasan lokatanta,Tattabara da tsattsewa, da gaurakasuna kiyaye lokacin komowarsu.Amma mutanena ba su san dokokinaba.’ ”
8Ƙaƙa za ku ce, “Muna da hikima,Dokar Ubangiji tana tare da mu”?Ga shi kuwa, alkalamin ƙarya namagatakarda, ya yi ƙarya.
9Za a kunyatar da masu hikima.Za su tsorata, za a kuma tafi da su.Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji.Wace hikima suke da ita?
10Saboda haka zan ba da matansu gawaɗansu,Gonakinsu kuma ga waɗanda sukecinsu da yaƙi,Saboda tun daga ƙarami har zuwababbaKowannensu yana haɗamar cinmuguwar riba,Tun daga annabawa zuwa firistociKowannensu aikata ha'inci yake yi.
11Sun warkar da raunin mutanenasama sama,Suna cewa, “Lafiya, lafiya,” alhalikuwa ba lafiya.
12Ko sun ji kunyaSa'ad da suka aikata ayyuka masubanƙyama?A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan,Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba.Domin haka za su faɗi tare dafāɗaɗɗu,Sa'ad da na hukunta su, za a ci su dayaƙi.Ni Ubangiji na faɗa.
13“Ni Ubangiji na ce,‘Sa'ad da zan tattara su kamaramfanin gona,Sai na tarar ba 'ya'ya a kurangarinabi,Ba 'ya'ya kuma a itacen ɓaure,Har ganyayen ma sun bushe.Abin da na ba su kuma ya kuɓucemusu.Ni Ubangiji na faɗa.’ ”
14Mutanen Urushalima sun ce,“Don me muke zaune kawai?Bari mu tattaru, mu tafi cikingaruruwa masu garu,Mu mutu a can,Gama Ubangiji Allahnmu yaƙaddara mana mutuwa,Ya ba mu ruwan dafi,Domin mun yi masa laifi.
15Mun sa zuciya ga salama, amma balafiya,Mun sa zuciya ga lokacin samunwarkewa,Amma sai ga razana!
16Daga Dan, an ji firjin dawakai.Dakan ƙasar ta girgiza sabodahaniniyar ingarmunsu.Sun zo su cinye ƙasar duk da abinda suke cikinta,Wato da birnin da mazaunacikinsa.”
17“Ni Ubangiji na ce, ‘Zan aiko mukuda macizai, da kāsā,Waɗanda ba su da makari,Za su sassare ku.’ ”
18Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa,Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!
19Ku ji kukan jama'ata ko'ina aƙasar,“Ubangiji, ba shi a Sihiyonane?Sarkinta ba ya a cikinta ne?”Ubangiji ya ce,“Me ya sa suka tsokane ni dasassaƙaƙƙun gumakansu,Da baƙin gumakansu?”
20Mutane suna ta cewa,“Damuna ta ƙare, kaka kuma tawuce,Amma ba a cece mu ba.”
21Raunin da aka yi wa jama'ata,Ya yi wa zuciyata rauni.Ina makoki, tsoro kuma ya kama niƙwarai.
22Ba abin sanyayawa a Gileyad ne?Ba mai magani a can ne?Me ya sa ba a warkar da jama'ataba?