Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
31 verses
1“Ku bi titunan Urushalima ko'ina!Ku dudduba ku lura!Ku bincika kowane dandali, ku gani,Ko za ku iya samun ko mutum ɗayaMai aikata adalci, mai son gaskiya,Sai in gafarta mata.
2Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse daran Ubangiji,’Duk da haka rantsuwar ƙarya sukeyi.”
3Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiyakake so ba?Ka buge su, amma ba su yi nishi ba,Ka hore su, amma sun ƙi horuwa,Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse,Sun ƙi tuba.
4Sai na ce,“Waɗannan mutane ba su da kirki,Ba su da hankali,Ba su san hanyar Ubangiji,Ko shari'ar Allahnsu ba.
5Zan tafi wurin manyan mutane, in yimusu magana,Gama sun san nufin Ubangiji, dashari'ar Allahnsu.”Amma dukansu sun ƙi yardaUbangiji ya mallake su,Suka ƙi yi masa biyayya.
6Domin haka zaki daga kurmi zaikashe su,Kyarkeci kuma daga hamada zaihallaka su.Damisa tana yi wa biranensukwanto,Duk wanda ya fita daga cikinsu sai ayayyage shi,Domin laifofinsu sun yi yawa,Karkacewarsu babba ce.
7“Don me zan gafarce ki?'Ya'yanki sun rabu da ni,Sun yi rantsuwa da gumaka,Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,Suka yi karuwanci, suka ɗungumazuwa gidajen karuwai,
8Kamar ƙosassun ingarmu suke,masu jaraba,Kowa yana haniniya, yana nemanmatar maƙwabcinsa.
9Ba zan hore su saboda waɗannanabubuwa ba?Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wakaina fansa a kan wannanal'umma ba?
10Ku haura, ku lalatar da gonarkurangar inabinta,Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,Ku sassare rassanta,Gama su ba na Ubangiji ba ne.
11Gama mutanen Isra'ila da mutanenYahuzaSun zama marasa aminci a gare ni.Ni Ubangiji na faɗa.”
12Sun yi ƙarya a kan Ubangiji,Suka ce, “Ba abin da zai yi,Ba wata masifa da za ta same mu.Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwaba.
13Annabawa holoƙo ne kawai,Maganar ba ta cikinsu.Haka za a yi da su!”
14Saboda haka Ubangiji Allah MaiRunduna ya ce,“Domin sun hurta wannan magana,Ga shi, zan sa maganata a bakinka tazama wuta,Waɗannan mutane kuwa su zamaitace,Wutar za ta cinye su.
15“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, inakawo mukuWata al'umma daga nesa,” in jiUbangiji,“Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tunzamanin dā.Al'umma wadda ba ku san harshentaba,Ba za ku fahimci abin da suke faɗaba.
16Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabarine,Dukansu jarumawa ne.
17Za su cinye amfanin gonakinku daabincinku.Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza.Za su cinye garkunanku na tumaki,da na awaki, da na shanu,Za su kuma cinye 'ya'yan inabinkuda na ɓaurenku.Za su hallaka biranenku masu kagarada takobi, waɗanda kuke fariya dasu.
18“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.
19“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ Sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”
20“Ka sanar wa zuriyar Yakubu dawannan,Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, kace,
21‘Ku ji wannan, ya ku wawaye,marasa hankali,Kuna da idanu, amma ba ku gani,Kuna da kunnuwa, amma ba kuji.’ ”
22Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsoronaba?Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?Ni ne na sa yashi ya zama iyakarteku,Tabbatacciyar iyaka, wadda ba tahayuwa,Ko da yake raƙuman ruwa za su yihauka, ba za su iya haye ta ba,Ko da suna ruri, ba za su iya wuce taba.
23Amma mutanen nan suna da taurinzuciya, masu halin tayarwa ne,Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.
24A zuciya ba su cewa,‘Bari mu ji tsoron UbangijiAllahnmuWanda yake ba mu ruwan sama akan kari,Na kaka da na bazara,Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
25Laifofinku sun raba ku da waɗannanabubuwa.Zunubanku kuma sun hana kusamun alheri.
26“Gama an sami mugaye, a cikinjama'ata,Suna kwanto kamar masu kafaashibta.Sun ɗana tarko su kama mutane.
27Kamar kwando cike da tsuntsaye,Haka nan gidajensu suke cike da cinamana,Don haka suka zama manya, sukasami dukiya.
28Sun yi ƙiba, sun yi bul- bul,Ba su da haram a kan aikatamugunta,Ba su yi wa marayu shari'ar adalci,don kada su taimake su.A wajen shari'a ba su bin hakkinmatalauta.
29“Ba zan hukunta su sabodawaɗannan abubuwa ba?Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kanal'umma irin wannan ba?
30“Abin banmamaki da bantsoroYa faru a ƙasar.
31Annabawa sun yi annabcin ƙarya,Firistoci kuma sun yi mulki da ikonkansu,Mutanena kuwa suna so haka!Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me zaku yi?”