Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
30 verses
1“Ya ku mutanen Biliyaminu, kugudu neman mafaka,Daga cikin Urushalima!Ku busa ƙaho a Tekowa,Ku ba da alama a Bet-akkerem,Gama masifa da babbar halaka sunfito daga arewa.
2Ya Sihiyona, ke kyakkyawarmakiyaya ce, zan hallaka abin dakika hahhaifa.
3Makiyaya da garkunansu za su zowurinki,Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.
4Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa matada yaƙi!Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakarrana!’Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, garana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.
5Mu tashi mu fāɗa mata da dare,Mu lalatar da fādodinta.’ ”
6Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ku sassare itatuwanta,Ku tula ƙasa kewaye daUrushalima,Dole in hukunta wannan birnisaboda ba kome cikinsa saizalunci,
7Kamar yadda rijiya take da ruwagarau,Haka Urushalima take damuguntarta,Ana jin labarin kama-karya da nahallakarwa a cikinta,Kullum akwai cuce-cuce, da raunukaa gabana,
8Ku ji faɗaka, ya ku mutanenUrushalima,Don kada a raba ni da ku,Don kada in maishe ku kufai,Ƙasar da ba mazauna ciki.”
9Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Za a kalace ringin Isra'ila sarai,kamar yadda ake wa inabi,Ka miƙa hannunka a kan rassantakamar mai tsinkar 'ya'yaninabi.”
10Da wa zan yi magana don in faɗakarda shi, don su ji?Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, suji,Ga shi, maganar Ubangiji kuwa tazama abin ba'a a gare su,Ba su marmarinta.
11Don haka ina cike da fushinUbangijiNa gaji da kannewa.Ubangiji ya ce,“Zan kwararo fushi kan yara da suke atiti.Da kuma kan tattaruwar samari.Za a ɗauke mata da miji duka biyu,Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufatukub-tukub.Za a ba waɗansu gidajensu, dagonakinsu, da matansu,Gama zan nuna ikona in hukuntamazaunan ƙasar.
12[...]
13Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,Kowannensu yana haɗama ya ciƙazamar riba,Har annabawa da firistoci,Kowannensu ya shiga aikata rashingaskiya.
14Sun warkar da raunin mutanenasama sama,Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhalikuwa ba lafiya.
15Sun ji kunya sa'ad da suka aikataabubuwan banƙyama?Ba su ji kunya ba ko kaɗan.Ko gezau ba su yi ba,Don haka za su fāɗi tare dafāɗaɗɗu,Sa'ad da na hukunta su, za ahamɓarar da su.Ni Ubangiji na faɗa.”
16Haka Ubangiji ya ce,“Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba,Ku nemi hanyoyin dā, inda hanyamai kyau take,Ku bi ta, don ku hutar darayukanku.Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’
17Na sa muku matsara cewa, in kun jian busa ƙaho ku kula!Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’
18“Don haka, ku ji, ya ku al'ummai,Ku sani, ku taron jama'a,Don ku san abin da zai same ku.
19Ki ji, ya ke duniya,Ga shi, ina kawo masifa a kanwannan jama'a,Sakayyar ƙulle-ƙullensu,Don ba su kula da maganata ba,Sun ƙi dokokina.
20Da wane nufi kuke kawo mini turaredaga Sheba,Ko raken da kuke kawowa dagaƙasa mai nisa?Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawaba,Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinkuba.
21Don haka, ni Ubangiji na ce,Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannanjama'a,Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi.Iyaye tare da 'ya'yansu, damaƙwabci,Do abokansu za su lalace.”
22Haka Ubangiji ya ce,“Ga shi, jama'a tana fitowa dagaƙasar arewa.Babbar al'umma ce,Ta yunƙuro tun daga manisantanwurare na duniya.
23Suna riƙe da baka da māshi,Mugaye ne marasa tausayi,Motsinsu kamar ƙugin teku ne.Suna haye a kan dawakai,A jere kamar wanda ya yi shirinyaƙiGāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”
24Mutanen Urushalima sun ce,“Mun ji labarin yaƙin,Hannuwanmu suka yi rauni.Azaba ta kama mu,Ciwo irin na mai naƙuda.
25Kada ku fita zuwa gona,Kada kuma ku yi yawo a kanhanya,Gama abokin gāba yana da takobi,Razana a kowane sashi.”
26“Ya mutanena, ku sa tufafin makoki,Ku yi birgima cikin toka,Ku yi makoki mai zafi irin wandaakan yi wa ɗa tilo,Gama mai hallakarwa zai auko mananan da nan.”
27Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Na maishe ka mai aunawa da maijarraba mutanenaDomin ka sani, ka aunaal'amuransu,
28Su duka masu taurinkai ne, 'yantawaye,Suna yawo suna baza jita-jita.Su tagulla ne da baƙin ƙarfe,Dukansu lalatattu ne.
29Ana zuga da ƙarfi,Dalma ta ƙone,Tacewar aikin banza ne,Gama ba a fitar da mugaye ba.
30Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfane,Gama ni na ƙi su.”