Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
20 verses
1Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.
2Ku dattawa, ku kasa kunne,Bari kowa da kowa da yake cikinYahuza, ya kasa kunne.Wani abu mai kamar wannan ya taɓafaruwa a lokacinku,Ko a lokacin kakanninku?
3Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa,'Ya'yanku kuma su faɗa wa'ya'yansu,'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsaramai zuwa.
4Abin da ɗango ya bari fara ta ci,Abin da fara ta bari burduduwa taci.
5Ku farka, ku yi ta kuka, kubugaggu,Ku yi kuka, ku mashayan ruwaninabi,An lalatar da 'ya'yan inabinDa ake yin sabon ruwan inabi da su.
6Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,Tana da ƙarfi, ba ta kumaƙidayuwa,Haƙoranta suna da kaifi kamar nazaki.
7Ta lalatar da kurangar inabinmu,Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.Ta gaigaye ɓawo duka,Saboda haka rassan sun zama farifat.
8Ya jama'a, ku yi kukaKamar yarinyar da take makokinrasuwar saurayinta.
9Ba hatsi ko ruwan inabinDa za a yi hadaya da su cikinHaikalin.Firistoci masu miƙa wa Ubangijihadaya suna makoki.
10Ba kome a gonaki,Ƙasa tana makoki,Domin an lalatar da hatsin,'Ya'yan inabi sun bushe,Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.
11Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,Ku yi kuka, ku da kuke lura dagonakin inabi,Gama alkama, da sha'ir,Da dukan amfanin gonaki sunlalace.
12Kurangar inabi ta bushe,Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,Rumman, da dabino, da gawasa,Da dukan itatuwan gonaki sunbushe.Murna ta ƙare a wurin mutane.
13Ya ku firistoci masu miƙa hadayu abagaden Ubangiji,Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka!Ku shiga Haikali, ku kwana,Kuna saye da tufafin makoki,Gama ba hatsi ko ruwan inabi da zaa yi hadaya da su,A cikin Haikalin Allahnku.
14Ku sa a yi azumi,Ku kira muhimmin taro.Ku tara dattawa da dukan mutanenƙasarA Haikalin Ubangiji Allahnku,Ku yi kuka ga Ubangiji.
15Taku ta ƙare a wannan rana!Gama ranar Ubangiji ta kusa,Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.
16An lalatar da amfanin gonaki a kanidonmu,Ba murna a Haikalin Allahnmu.
17Itatuwa sun mutu a busasshiyarƙasa,Ba hatsin da za a adana a rumbu,Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.
18Dabbobi suna nishi!Garkunan shanu sun ruɗeDomin ba su da makiyaya.Garkunan tumaki da awaki kumasuna shan azaba.
19Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji,Domin ciyayi da itatuwa sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.
20Har ma namomin jeji suna kuka agare ka,Domin rafuffuka sun bushe,Ciyayi kuma sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.