Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Ki tattara sojojinki, gama ankewaye mu da yaƙi.Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ilada sanda.
2“Baitalami cikin Efrata,Wadda kike 'yar ƙarama a cikinkabilar Yahuza,Amma daga cikinki wani zai fitowanda zai sarauci Isra'ilaWanda asalinsa tun fil azal ne.”
3Domin haka zai yashe su,Sai lokacin da wadda take naƙuda tahaihu.Sa'an nan sauran 'yan'uwansaZa su komo wurin mutanen Isra'ila.
4Shi kuwa zai tashi ya ciyar dagarkensa da ƙarfin Ubangiji,Da ɗaukakar sunan UbangijiAllahnsa.Za su kuwa zauna lafiya,Gama zai zama mai girma cikinduniya duka.
5Zai zama salamarmu.Sa'ad da kuma Assuriyawa za sukawo mana yaƙi,Za su tattake kagaranmu,Za mu sa makiyaya bakwai dashugabanni takwas su yi gāba dasu.
6Za su mallaki ƙasar Assuriya datakobi,Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod dazararren takobi,Zai cece mu daga hannunBa'assuriye,Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmuyaƙi,Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.
7Sa'an nan ringin Yakubu zai zamarwa mutaneKamar raɓa daga wurin Ubangiji,Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire,Wanda ba ya jinkiri ko ya jiramutane.
8Ringin Yakubu kuma zai zamar waal'umman duniya,Kamar yadda zaki yake a tsakaninnamomin jeji,Kamar kuma yadda zaki yake atsakanin garkunan tumaki,Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakantattaka,Ya yi kacakaca da su,Ba wanda zai cece su.
9Za a ƙarfafa hannunka a kanmaƙiyanka,Za a datse maƙiyanka duka.
10“A wannan rana, ni Ubangiji na ce,Zan kashe dawakanku, in hallakakarusanku.
11Zan shafe biranen ƙasarku,In rushe garunku.
12Zan kawar da maita daga ƙasarku,Ba za ku ƙara samun bokaye ba.
13Zan sassare siffofinku daginshiƙanku,Ba za ku ƙara sunkuya wa aikinhannuwanku ba.
14Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarotdaga cikinku,Zan hallaka biranenku.
15Da fushi da hasala zan yi sakayyaA kan al'umman da ba su yi biyayyaba.”