Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
16 verses
1“Ku ji abin da ni Ubangiji nake cewa,Tashi ku gabatar da ƙararku agaban duwatsu,Ku bar tuddai su ji muryarku.
2“Ku duwatsu da madawwaman tussan duniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi muku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.
3“Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!
4Gama na fito da ku daga ƙasar Masar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.
5Ya ku jama'ata, ku tunaDa abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla,Da yadda Bal'amu ɗan Beyor yaamsa masa,Da abin da ya faru daga Shittim, harzuwa Gilgal,Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”
6Da me zan zo gaban Ubangiji,In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama?Ko in zo gabansa da maraƙi banaɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa?
7Ubangiji zai yi murna da raguna dubbaiKo kuwa da kogunan mai dubbai?Zan ba da ɗan farina ne donlaifina?Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina?
8Ya kai mutum, ya riga ya nunamaka abin da yake mai kyau.Abin da Ubangiji yake so gare ka,shi neKa yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri,Ka bi Allah da tawali'u.
9Ubangiji yana kira ga birnin.Hikima ce ƙwarai a ji tsoron sunanka.“Ki ji ya kabila, wa ya sa mikilokacinki?
10Ba zan manta da dukiya ta muguntaa gidan mugu ba,Ba kuwa zan manta da bugaggenmudun awo ba.
11Zan kuɓutar da mutum mai ma'aunina cutaDa ma'aunin ƙarya?
12Attajiran birnin sun cika zalunci,Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,Harshensu na yaudara ne.
13Domin haka zan buge ku da ciwo,In maishe ku kufai saboda zunubanka.
14Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,Yunwa za ta kasance a cikinku,Za ku tanada, amma ba zai tanadu ba,Abin da kuma kuka tanada zan baiwa takobi.
15Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba.Za ku matse 'ya'yan zaitun, ammaba za ku shafa mansa ba,Za ku kuma matse 'ya'yan inabi,amma ba za ku sha ruwansa ba.
16Domin kun kiyaye dokokin Omri,Kun bi halin gidan Ahab,Kun kuma bi shawarwarinsu.Domin haka zan maishe ku kufai,In mai da ku abin dariya,Za ku sha raini a wurin mutanena.”