Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.
2Ubangiji Allah mai kishi ne, maisakayya,Ubangiji mai sakayya ne, maihasala.Ubangiji yakan ɗauki fansa a kanmaƙiyansa.Yana tanada wa maƙiyansa fushi.
3Ubangiji mai jinkirin fushi ne,Mai Iko Dukka.Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifiba.Hanyarsa tana cikin guguwa da cikinhadiri,Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.
4Yakan tsauta wa teku, sai teku taƙafe.Yakan busar da koguna duka.Bashan da Karmel sukan bushe,Tohon Lebanon yakan yanƙwane.
5Duwatsu sukan girgiza a gabansa,Tuddai kuma su narke.Duniya ta murtsuke a gabansa,Da dukan mazauna a cikinta.
6Wa zai iya tsaya wa fushinsa?Wa kuma zai iya daurewa dahasalarsa?Yana zuba hasalarsa mai kama dawuta,Duwatsu sukan farfasu a gabansa.
7Ubangiji mai alheri ne,Shi mafaka ne a ranar wahala.Ya san waɗanda suke fakewa a gareshi.
8Zai shafe maƙiyansa da ambaliyarruwa,Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwacikin duhu.
9Me kuke ƙullawa game da Ubangiji?Ubangiji zai wofintar da abin nan dakuke ƙullawa,Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.
10Suna maye da abin shansu,Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya,Da busasshiyar ciyawa.
11Daga cikinki wani ya fito,Wanda ya ƙulla wa Ubangijimakirci,Ya ƙulla shawara marar amfani.
12Ni Ubangiji na ce,“Ko da yake suna da ƙarfi, sunakuma da yawa,Za a datse su, su ƙare.Ko da yake na wahalar da kai,Ba zan ƙara wahalar da kai ba.
13Yanzu zan karya karkiyarsa dagawuyanka,Zan kuma tsinke sarƙarta.”
14Ubangiji ya riga ya yi umarni akanka cewa,“Sunanka ba zai ci gaba ba,Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofiDa siffofi na zubi daga gidangumakanka.Zan shirya maka kabari, gama kairainanne ne.”
15Duba a kan duwatsu, ƙafafunwanda yake kawo albishir,Wanda yake shelar salama!Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka,Ka kuma cika wa'adodinka.Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yigāba da kai ba,An datse shi ƙaƙaf.