Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
13 verses
1Wanda yake farfashewa ya aukomaka,Sai ka sa mutane a kagara, a yitsaron hanya,Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinkaduka.
2Gama Ubangiji zai mayar waYakubu da darajarsa kamar taIsra'ila.Ko da masu washewa sun washe su,Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.
3Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.Da ya shirya tafiya,Karusai suna walƙiya kamarharshen wuta,Ana kaɗa mashi da bantsoro.
4Karusai sun zabura a tituna ahaukace.Suna kai da kawowa a dandali,Suna walwal kamar jiniya,Suna sheƙawa a guje kamarwalƙiya.
5Sai aka kira shugabanni,Suka zo a guje suna tuntuɓe,Suka gaggauta zuwa garu,Suka kafa kagara.
6An buɗe ƙofofin kogi,Fāda ta rikice.
7An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,'Yan matanta suna makoki, sunakuka kamar kurciyoyi,Suna bugun ƙirjinsu.
8Nineba tana kama da tafki wandaruwansa yake zurarewa,Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”Amma ba wanda ya waiga.
9A washe azurfa!A washe zinariya!Dukiyar ba ta da adadi,Akwai dukiya ta kowane iri.
10Nineba ta halaka! ta lalace, ta zamakufai!Zukata sun narke, gwiwoyi sunakaɗuwa!Kwankwaso yana ciwo,Fuskoki duka sun kwantsare!
11Ina kogon nan na zakoki,Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki,Inda zaki da zakanya dakwiyakwiyansu sukan tafi,Su tsere daga fitina?
12Zaki ya kashe abin da ya ishikwiyakwiyansa.Ya kaso wa zakanyarsa abin da yaishe ta.Ya cika kogonsa da ganima.
13“Ga shi, ina gāba da ke. Ni UbangijiAllah Mai Runduna na faɗa.Zan ƙone karusanki,Takobi kuwa zai karkashe sagarunzakokinki,Zan hana miki ganima a duniya.Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunkiba.”