Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
19 verses
1Kaiton birnin jini,Wanda yake cike da ƙarairayi daganima,Da waso kuma ba iyaka!
2Ku ji amon bulala da kwaramniyarƙafafu,Da sukuwar doki da girgizar karusai!
3Sojojin dawakai suna kai sura,Takuba suna walƙiya, māsu sunaƙyalƙyali.Ga ɗumbun kisassu, da tsibingawawwaki,Matattu ba su ƙidayuwa,Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!
4Ya faru saboda yawan karuwancinNineba kyakkyawa mai daɗinbaki,Wadda ta ɓad da al'umman duniyada karuwancinta,Ta kuma ɓad da mutane da daɗinbakinta.
5Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Inagāba da ke,Zan kware fatarinki a idonki,Zan sa al'ummai da mulkoki su dubitsiraicinki.
6Zan watsa miki ƙazanta,In yi miki wulakanci,In maishe ki abin raini.
7Dukan waɗanda za su dube kiZa su ja da baya su ce,‘Nineba ta lalace, wa zai yi kukadominta?’A ina zan samo miki waɗanda za suta'azantar da ke?”
8Kin fi No ne?Wadda take a bakin Nilu,Wadda ruwa ya kewaye ta?Teku ce kagararta.Ruwa ne kuma garunta.
9Habasha da Masar su ne ƙarfintamarar iyaka,Fut da Libiya su ne kumamataimakanta.
10Duk da haka an tafi da ita, an kai tacikin bauta.An fyaɗa ƙanananta a ƙasa,An yi kacakaca da su a kowacemararraba.An jefa kuri'a a kan manyanmutanenta,Aka ɗaure dukan manyan mutanentada sarƙoƙi.
11Ke Nineba kuma za ki bugu,Za a ɓoye ki.Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.
12Dukan kagaranki suna kama daitatuwan ɓaure,Waɗanda 'ya'yansu suka harba.Da an girgiza sai su faɗo a bakin maisha.
13Sojojinki kamar mata suke atsakiyarki!An buɗe wa maƙiyanki ƙofofinƙasarki.Wuta za ta cinye madogaranƙofofinki.
14Ki tanada ruwa domin za a kewayeki da yaƙi!Ki ƙara ƙarfin kagaranki!Ki tafi kududdufi, ki kwaɓa laka!Ki ɗauki abin yin tubali!
15A can wuta za ta cinye ki,Takobi zai sare ki,Zai cinye ki kamar fara.Ki riɓaɓɓanya kamar fara.Ki kuma riɓaɓɓanya kamar ɗango.
16Kin yawaita 'yan kasuwanki suna dayawa fiye da taurari,Amma sun tafi kamar fara waɗandasukan buɗe fikafikansu su tashi, sutafi.
17Shugabanninki kamar ɗango suke,Manyan mutanenki kamarcincirindon fāra ne,Suna zaune a kan shinge a kwanakinsanyi,Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi sutafi,Ba wanda ya san inda suke.
18Ya Sarkin Assuriya, masu tsaronkasuna barci,Manyan mutanenka sunakwankwance,Mutanenka sun watse cikinduwatsu,Ba wanda zai tattaro su.
19Ba abin da zai rage zafin rauninka,Rauninka ba ya warkuwa.Duk wanda ya ji labarinka, zai tafahannuwansaGama wane ne ba ka musguna waba?