Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
45 verses
1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
2Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
3Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.
5Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
6[...]
7Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.
8Zai cika alkawarinsa har abada,Alkawaransa kuma don dubban zamanai,
9Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.
10Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,
11“Zan ba ka ƙasar Kan'ana,Za ta zama mallakarka.”
12Jama'ar Ubangiji kima ne,Baƙi ne kuwa a ƙasar.
13Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,Daga wannan mulki zuwa wancan,
14Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.
15Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu,Kada ku cuci annabawana!”
16Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu,Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,
17Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa,Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.
18Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa,Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,
19Har kafin faɗar da ya yi, ta cika.Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.
20Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi,Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.
21Ya sa shi ya lura da mulkinsa,Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.
22Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma.Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.
23Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar,Ya zauna a ƙasar.
24Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa,Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.
25Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,Suka yi wa bayinsa munafunci.
26Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.
27Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.
28Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.
30Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.
31Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.
32Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.
33Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,Ya kakkarya itatuwansu.
34Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.
35Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa.Suka cinye dukan amfanin gonaki.
36Ya karkashe dukan 'ya'yan fari mazaNa dukan iyalan Masarawa.
37Sa'an nan ya bi da Isra'ilawa, suka fita,Suka kwashi azurfa da zinariya,Dukansu kuma ƙarfafa ne lafiyayyu.
38Masarawa suka yi murna da fitarsu,Gama sun tsoratar da su.
39Ya sa girgije ya yi wa jama'arsa inuwa,Da dare kuma wuta ta haskaka musu.
40Suka roƙa, sai aka ba su makware,Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.
41Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo,Yana gudu cikin hamada kamar kogi.
42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkiWanda ya yi wa bawansa Ibrahim.
43Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa,Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.
44Ya ba su ƙasar baƙi,Ya sa su gāje gonakinsu,
45Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa,Su kuma kiyaye umarninsa.Ku yabi Ubangiji!