Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
31 verses
1Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!
2Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.
3Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.Suna tasar mini ba dalili.
4Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,Har ina yi musu addu'a.
5Sukan sāka mini alheri da mugunta,Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.
6Ka zaɓi lalataccen mutum ya shara'anta maƙiyina,Ka sa ɗaya daga cikin maƙiyansaYa gabatar da ƙararsa.
7Ka sa a same shi da laifi a shari'ar da ake yi masa,Ka sa har addu'ar da yake yiTa zama babban laifi!
8Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan,Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!
9Ka sa 'ya'yansa su zama marayu,Matarsa kuwa ta zama gwauruwa!
10Ka sa 'ya'yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara.Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!
11Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwasheDukan abin da yake da shi.Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.
12Ka sa kada kowa ya yi masa alheri sam,Kada ka bar kowa ya lura da marayunsa.
13Ka sa dukan zuriyarsa su mutu,Har a manta da sunansa a tsara mai zuwa.
14Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa,Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.
15Ka tuna da zunubansu kullayaumin, ya Ubangiji,Amma su kansu a manta da su ɗungum!
16Gama mutumin nan bai taɓa tunanin yin alheri ba,Yakan tsananta wa talakawa, da matalauta, da kasassu, har ya kashe su.
17Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi!Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!
18Yakan la'antar a sawwaƙe kamar yadda yake sa tufafinsa.Ka sa la'antarwa da yake yiSu jiƙa shi kamar ruwa,Su shiga har ƙasusuwansa kamar mai,
19Su lulluɓe shi kamar tufa,Su kuma kewaye shi kamar ɗamara.
20Ya Ubangiji, ka sa haka,Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan,Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!
21Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni,Yadda ka alkawarta,Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.
22Ni talaka ne, matalauci,Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.
23Na kusa ɓacewa kamar inuwar maraice,An hurar da ni can kamar ƙwaro.
24Gwiwoyina sun yi suwu saboda rashin abinci,Jikina kuma ya rame, ba shi da ƙarfi.
25Sa'ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba'a,Suna kaɗa kai saboda raini.
26Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna,Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
27Ka sa maƙiyana su sani,Kai ne Mai Cetona.
28Watakila su la'anta ni,Amma kai za ka sa mini albarka,Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini.Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.
29Ka sa kunya ta rufe maƙiyana,Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.
30Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya.Zan yabe shi a taron jama'a,
31Saboda yakan kāre talaka,Domin ya cece shi daga waɗandaSuka sa masa laifin mutuwa.