Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina,“Zauna nan a damana,Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce,“Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka,Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.Kamar yadda raɓa take da sassafe,Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4Ubangiji ya yi muhimmin alkawari,Ba kuwa zai fasa ba!“Za ka zama firist har abadaBisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
5Ubangiji yana damanka,Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma,Ya rufe fagen fama da gawawwaki,Zai kori sarakunan duk duniya.
7Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya,Ya wartsake ya sami ƙarfi.Zai yi tsayawar nasara.