Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
4 verses
1Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka,A Sama inda kake mulki.
2Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa,Baranya kuma ga uwargijiyarta,Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu,Har mu sami jinƙanka.
3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,An gwada mana wulakanci matuƙa!
4Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a,Azzalumai masu girmankai sun raina mu!