Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
8 verses
1Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,Da me zai faru?Ba da amsa, ya Isra'ila!
2“Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,
3Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,Saboda zafin fushi da suke yi da mu,
4Da rigyawa ta kwashe mu,Da ruwa yi ci mu,
5Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”
6Sai mu gode wa Ubangiji,Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.
7Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta,Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!
8Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa,Shi wanda ya yi sama da duniya.