Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Sa'ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona,Sai abin ya zama kamar mafarki!
2Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki,Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce,“Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”
3Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu,Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!
4Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmuKamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,
5Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe,Su tattara albarkar kaka da farin ciki!
6Su waɗanda suka yi kuka a sa'ad da suka fita suna ɗauke da iri,Za su komo ɗauke da albarkar kaka,Suna raira waƙa don farin ciki!