Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
5 verses
1Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,Aikin magina banza ne.Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.
2Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.
3'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji,Albarka ce ta musamman.
4'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsaKamar kibau suke a hannun mayaƙi.
5Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa!Faufau ba za a ci nasara a kansa ba,Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.