Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji,Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!
2Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka,Za ka yi farin ciki ka arzuta.
3Matarka za ta zama kamar kurangar inabiMai 'ya'ya a gidanka,'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitunSuna kewaye da teburinka.
4Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya,Hakika za a sa masa albarka kamar haka.
5Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona!Ya sa ka ga Urushalima ta arzutaDukan kwanakinka!
6Ya kuma sa ka ka ga jikokinka!Salama ta kasance ga Isra'ila!