Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
8 verses
1Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntarDa maƙiyanka suka tsananta maka da ita,Tun kana ƙarami!
2“Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,Tun ina ƙarami,Amma ba su yi nasara da ni ba.
3Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.
4Amma Ubangiji mai adalci,Ya 'yantar da ni daga bauta.”
5Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,A yi nasara da su a kuma kore su!
6Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.
7Ba wanda zai tattara ta,Ya ɗaure ta dami dami.
8Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce,“Ubangiji ya sa maka albarka!” ba,Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!”