Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?
2Har yaushe raina zai jure da shan wahala?Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?
3Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini,Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.
4Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba!Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.
5Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka,Zan yi murna gama za ka cece ni.
6Zan raira waƙa ga Ubangiji,Gama ya kyautata mini.