Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!”Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.
2Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane,Yă ga ko da akwai masu hikimaWaɗanda suke yi masa sujada.
3Amma dukansu sun koma baya,Su duka mugaye ne,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,Babu ko ɗaya.
4Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba?Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne?Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke zaman gari,Ba su yin addu'a gare ni.”
5Amma za su razana,Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.
6Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya,Saboda yana dogara ga Ubangiji.
7Ina addu'a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona!Sa'ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama'arsa,Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki,Jama'ar Isra'ila za su yi murna.