Hausa Holy Bible Wordproject Bible
3 verses
1Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma,Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!
2Yana kama da man zaitun mai daraja,Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa,Har zuwa wuyan riganunsa.
3Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon,Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona.A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa,Rai na har abada.