Hausa Holy Bible Wordproject Bible
3 verses
1Ku zo mu yabi Ubangiji,Dukanku bayinsa,Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima,A cikin Haikalinsa da dare.
2Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali,Ku yabi Ubangiji!
3Ubangiji wanda ya yi sama da duniya,Ya sa muku albarka daga Sihiyona.