Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
9 verses
1A bakin kogunan BabilaMuka zauna muka yi ta kuka,Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.
2A rassan itatuwan wardi da suke kusa da muMuka rataye garayunmu.
3Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,Suka ce mana, “Ku yi mana shagaliDa waƙar da aka raira wa Sihiyona!”
4Kaƙa za mu raira waƙar UbangijiA baƙuwar ƙasa?
5Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,Idan na manta da ke, Urushalima!
6Da ma kada in ƙara iya raira waƙa,Idan na manta da ke,Idan ban tuna ke ceBabbar abar farin ciki ba!
7Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi,A ranar da aka ci Urushalima.Ka tuna da yadda suka ce,“A ragargaza ta har ƙasa!”
8Babila, za a hallaka ki!Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka mikiBisa ga abin da kika yi mana.
9Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jarirankiYă fyaɗa su a kan duwatsu!