Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Ubangiji makiyayina ne,Ba zan rasa kome ba.
2Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.
3Yana ba ni sabon ƙarfi.Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.
4Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,Gama kana tare da ni!Sandanka na makiyayi da kerenkaSuna kiyaye lafiyata.
5Ka shirya mini liyafaInda maƙiyana duk za su iya ganina,Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,Ka cika tanduna fal da mai.
6Hakika, alherinka da ƙaunarkaZa su kasance tare da ni muddin raina.Haikalinka zai zama gidana har abada.