Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
10 verses
1Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne,Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.
2Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa,Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.
3Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji?Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?
4Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani,Wanda ba ya yi wa gumaka sujada,Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.
5Ubangiji zai sa masa albarka,Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.
6Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.
7A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!
8Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!
9A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!
10Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!