Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
11 verses
1Ku yabi Ubangiji, ku alloli,Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.
2Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.
3An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.
4An ji muryar UbangijiA dukan ikonsa da zatinsa!
5Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul,Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.
6Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa,Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.
7Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.
8Muryarsa ta sa hamada ta girgiza,Ta girgiza hamadar Kadesh.
9Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu,Ta sa itatuwa su kakkaɓe,Sa'ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa,Aka ce, “Daukaka ga Allah!”
10Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi,Yana sarauta kamar sarki har abada.
11Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi,Ya sa musu albarka da salama.