Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
12 verses
1Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni,Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.
2Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna,Ka kuwa warƙar da ni.
3Ka dawo da ni daga lahira.Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa,Amma ka ceci raina.
4Ku raira yabo ga Ubangiji,Ku amintattun jama'arsa!Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata,Ku yi masa godiya!
5Fushinsa ba ya daɗewa,Alherinsa kuwa har matuƙa ne.Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,Amma a yi murna da safe.
6Ina zaune jalisan, na ce wa kaina,“Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”
7Kana yi mini alheri, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse.Amma sa'ad da ka ɓoye mini fuskarka,Sai in cika da tsoro.
8Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Ina roƙon taimakonka.
9Wane amfani za a samu daga mutuwata?Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari?Ko matattu suna iya yabonka?Za su iya shelar madawwamin alherinka?
10Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!Ka taimake ni, ya Ubangiji!
11Ka mai da baƙin cikinaYa zama rawar farin ciki,Ka tuɓe mini tufafin makoki,Ka sa mini na farin ciki.
12Don haka ba zan yi shiru ba,Zan raira maka yabo,Ya Ubangiji, kai ne Allahna,Zan gode maka har abada.