Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
8 verses
1Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji,Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!
2Suna magana a kaina, suna cewa,“Allah ba zai taimake shi ba!”
3Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari,Kana ba ni nasara,Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
4Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako,Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.
5Na kwanta na yi barci,Na kuwa tashi lafiya lau,Gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6Ba na jin tsoron dubban abokan gābaWaɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.
7Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,Ka hallakar da dukan mugaye.
8Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,Bari yă sa wa jama'arsa albarka!