Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
9 verses
1Ku yi tāfi saboda farin ciki,Ya ku jama'a duka!Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!
2A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka,Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.
3Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i,Ya sa muka yi mulkin al'ummai,
4Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune,Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsaWadda yake ƙauna.
5Allah ya hau kan kursiyinsa!Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,Lokacin da Ubangiji yake hawa!
6Ku raira yabbai ga Allah,Ku raira yabbai ga sarkinmu!
7Allah sarki ne na duniya duka,Ku yabe shi da waƙoƙi!
8Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki,Yana mulkin al'ummai,
9Masu mulkin al'ummai suka tattaruTare da jama'ar Allah na Ibrahim.Allah shi ne garkuwar jarumawa,Yana mulkin duka!