Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
14 verses
1Ubangiji mai girma ne,Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu,A kan tsattsarkan dutsensa.
2Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,Mai kyan gani ne na Allah,Birnin babban Sarki.Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!
3Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,A kagarar birnin.
4Sarakuna suka tattaru,Suka zo Dutsen Sihiyona,
5Da suka gan shi sai suka yi mamaki,Suka tsorata suka gudu.
6Tsoro ya kama su suka razana,Kamar mace wadda take gab da haihuwa.
7Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.
8Mun ji labarin waɗannan al'amura,Yanzu kuwa mun gan suA birnin Allahnmu, Mai Runduna,Zai kiyaye birnin lafiya har abada.
9A cikin Haikalinka, ya Allah,Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.
10A ko'ina jama'a suna yabonka,Sunanka ya game duniya duka.Kana mulki da adalci.
11Bari jama'ar Sihiyona su yi murna!Gama kana shari'a ta gaskiya,Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.
12Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona,Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.
13Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta,Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa,
14Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin,Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.