Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
5 verses
1Ka cece ni, ya Allah!Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
2Ka sa masu so su kashe ni,A ci nasara a kansu, su ruɗe!Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!
3Ka sa waɗanda suke mini ba'aSu razana sabili da fāɗuwarsu!
4Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare kaSu yi murna, su yi farin ciki!Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonkaKullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
5Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.Kai ne mataimakina da Mai Cetona,Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!