Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
72 verses
1Ku kasa kunne ga koyarwata, ya ku jama'ata,Ku kula da abin da nake faɗa.
2Zan yi magana da ku,In faɗa muku asirai na dā,
3Abubuwan da muka ji muka kuwa sani,Waɗanda kakanninmu suka faɗa mana.
4Ba za mu ɓoye waɗannan abubuwa daga 'ya'yanmu ba,Amma za mu faɗa wa tsara mai zuwaLabarin ikon Ubangiji, da manya manyan ayyukansa,Da abubuwan banmamaki waɗanda ya aikata.
5Ya ba da dokoki ga jama'ar Isra'ila,Da umarnai ga zuriyar Yakubu.Ya ba kakanninmu ka'idodi,Don su koya wa 'ya'yansu dokokinsa,
6Saboda tsara mai zuwa ta koye su,Su kuma su koya wa 'ya'yansu.
7Ta haka su ma za su dogara ga Allah,Ba za su manta da abin da ya yi ba,Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.
8Kada su zama kamar kakanninsu,Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya.Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,Ba su kuwa yi masa aminci ba.
9Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibauSuka gudu a ranar yaƙi.
10Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,Sun ƙi biyayya da dokokinsa.
11Sun manta da abin da ya aikata,Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.
12Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujizaA filin Zowan a ƙasar Masar.
13Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.
14Da rana sai ya bi da su da girgije,Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.
15Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.
16Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse,Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.
17Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi,A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.
18Da gangan suka jarraba Allah,Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.
19Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?
20Gaskiya ce, ya bugi dutse,Ruwa kuwa ya fito a yalwace,Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”
21Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su,Ya aukar wa jama'arsa da wuta,Fushinsa ya haɓaka a kansu,
22Saboda ba su amince da shi ba,Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.
23Amma ya yi magana da sararin sama,Ya umarci ƙofofinsa su buɗe,
24Ya ba su tsaba daga sama,Da ya sauko musu da manna, su ci.
25Ta haka suka ci abincin mala'iku.Allah ya ba su iyakar abin da za su iya ci.
26Sa'an nan sai ya sa iskar gabas ta hura,Da ikonsa kuma ya sa iskar kudu ta tashi.
27Ya aika da tsuntsaye bisansu kamar ƙura,Yawansu kamar yashi a gaɓa,
28Sai suka fāɗo a zango,Kewaye da alfarwai ko'ina.
29Sai mutane suka ci suka ƙoshi,Allah ya ba su iyakar abin da suke bukata.
30Amma sa'ad da suke cikin ci,Tun ba su ƙoshi ba,
31Sai Allah ya yi fushi da su.Ya karkashe ƙarfafan mutane,Da samarin Isra'ila na gaske!
32Ko da yake ya aikata mu'ujizai da yawa,Duk da haka jama'a suka ci gaba da yin zunubi,Ba su kuwa gaskata shi ba.
33Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi,Bala'i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.
34Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu,Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba,Suka yi addu'a sosai a gare shi.
35Sun tuna, ashe, Allah ne mai kiyaye su,Sun tuna Maɗaukaki shi ne Mai Fansarsu.
36Amma maganganunsu duka ƙarya ne,Dukan abin da suka faɗa kuwa daɗin baki ne kawai.
37Ba su yi masa biyayya ba,Ba su yi aminci game da alkawarin da suka yi da shi ba.
38Amma Allah ya yi wa jama'arsa jinƙai,Ya gafarta zunubansu,Bai hallaka su ba.Sau da yawa yakan kanne fushinsa,Ya dakatar da hasalarsa.
39Yakan tuna su mutane ne kawai,Kamar iskar da take hurawa ta wuce.
40Sau da yawa suka tayar masa a hamada.Sau da yawa suka sa shi yin ɓacin rai!
41Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai,Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra'ila yin fushi.
42Suka manta da ikonsa mai girma.Suka manta da lokacin da ya cece su daga abokan gābansu,
43Lokacin da ya aikata manyan ayyuka da mu'ujizaiA filin Zowan, ta ƙasar Masar.
44Ya mai da koguna su zama jini,Masarawa kuwa suka kasa sha daga rafuffukansu.
45Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su,Kwaɗi suka lalata filayensu.
46Ya aiko da gamzari don su ci amfanin gonakinsu,Ya aiko da ɗango su lalata gonakinsu.
47Ya kashe kurangar inabinsu da ƙanƙara,Ya kuma kashe itatuwan ɓaurensu da jaura.
48Ya karkashe shanunsu da ƙanƙara,Ya kuma karkashe garkunan tumakinsu da na awakinsu da tsawa.
49Ya buge su da fushinsa mai zafi, da hasalarsa,Ya sa su damuwa ƙwarai,Da ya aiko da mala'iku masu hallakarwa.
50Bai kanne fushinsa ba,Bai bar su da rai ba,Amma ya karkashe su da annoba.
51Ya karkashe 'yan fari mazaNa dukan iyalan da suke Masar.
52Sa'an nan ya bi da jama'arsaKamar makiyayi, ya fito da su,Ya yi musu jagora cikin hamada.
53Ya bi da su lafiya, ba su kuwa ji tsoro ba,Amma teku ta cinye abokan gābansu.
54Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa,Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.
55Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako,Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila,A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.
56Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye,Suka jarraba shi.Ba su kiyaye dokokinsa ba,
57Amma suka yi tawaye da rashin aminciKamar kakanninsu,Kamar kiban da aka harba da tanƙwararren baka,Waɗanda ba su da tabbas.
58Suka sa shi ya yi fushi sabodaMasujadansu na arnanci.Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.
59Allah ya yi fushi sa'ad da ya ga haka,Don haka ya rabu da jama'arsa ɗungum.
60Ya bar alfarwarsa da take a Shilo,Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.
61Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari,Inda aka ga ikonsa da darajarsa,
62Ya ji fushi da jama'arsa,Ya bar abokan gābansu su karkashe su.
63Aka karkashe samari a cikin yaƙi,'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.
64Aka karkashe firistoci da takuba,Matansu ba su yi makoki dominsu ba.
65Daga bisani sai Ubangiji ya tashiKamar wanda ya farka daga barci,Kamar jarumi wanda ya bugu da ruwan inabi.
66Ya tura abokan gābansa baya,Da mummunar kora mai bankunyaDa ba za su sāke tashi ba.
67Ubangiji ya rabu da zuriyar Yusufu,Bai kuma zaɓi kabilar Ifraimu ba.
68A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza.Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.
69A can ya gina Haikalinsa,Kamar wurin zamansa a Sama.Ya kafa shi da ƙarfi kamar duniya,Tabbatacce a kowane lokaci.
70Ya zaɓi bawansa Dawuda,Ya ɗauko shi daga wurin kiwon tumaki,
71Ya ɗauko shi daga inda yake lura da 'yan raguna.Ya naɗa shi Sarkin Isra'ila,Ya naɗa shi makiyayin jama'ar Allah.
72Dawuda kuwa ya lura da su da zuciya ɗaya,Da gwaninta kuma ya bi da su.