Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
8 verses
1Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa,Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.
2Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a,Ku daina goyon bayan mugaye!
3Ku kāre hakkin talakawa da na marayu,Ku yi adalci ga matalauta,Da waɗanda ba su da mataimaki.
4Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,Ku cece su daga ikon mugaye!
5“Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!Kuna zaune cikin duhu,Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6Na faɗa muku, ku alloli ne,Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7Amma za ku mutu kamar kowane mutum,Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya,Dukan al'ummai naka ne.