Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
13 verses
1Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri,Ka sāke arzuta Isra'ila kuma.
2Ka gafarta wa jama'arka zunubansu,Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,
3Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.
4Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu,Ka daina jin haushinmu!
5Za ka yi fushi da mu har abada?Ba za ka taɓa hucewa ba?
6Ka daɗa mana ƙarfi, ka yarda ka sabunta ƙarfinmu,Mu kuwa, jama'arka, za mu yabe ka.
7Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,Ka taimake mu da cetonka.
8Ina kasa kunne ga abin da Ubangiji Allah yake cewa,Mu da muke mutanensa, ya alkawarta mana salama,Idan ba mu koma kan al'amuranmu na wauta ba.
9Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi,Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.
10Ƙauna da aminci za su sadu wuri ɗaya,Adalci da salama za su gamu.
11Amincin mutum zai yunƙura daga duniya, yă nufi sama.Adalcin Allah kuwa zai dubo daga Sama.
12Ubangiji zai arzuta mu,Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.
13Adalci zai yi tafiya a gaban Ubangiji,Yă shirya masa tafarki.