Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
17 verses
1Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini,Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.
2Ka cece ni daga mutuwa, saboda ni mai aminci ne a gare ka,Ka cece ni saboda ni bawanka ne, ina kuwa dogara gare ka.
3Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.
4Ka sa bawanka yă yi murna, ya Ubangiji,Saboda addu'o'ina sun hau zuwa gare ka.
5Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara,Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.
6Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,Ka ji kukana na neman taimako!
7Nakan kira gare ka a lokacin wahala,Saboda kakan amsa addu'ata.
8Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji,Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.
9Dukan sauran al'umma da ka halittaZa su zo su rusuna har ƙasa a gabanka.Za su yabi girmanka,
10Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah,Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.
11Ya Ubangiji, ka koya mini abin da kake so in yi,Ni kuwa zan yi maka biyayya da aminci.Ka koya mini in bauta maka da zuciya ɗaya.
12Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji Allahna,Zan riƙa shelar girmanka har abada.
13Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni!Gama ka cece ni daga zurfin kabari.
14Masu girmankai sun tasar mini, ya Allah,Ƙungiyar mugaye tana ƙoƙari ta kashe ni,Mutanen da ba su kula da kai ba.
15Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna,Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.
16Ka juyo gare ni, ka yi mini jinƙai,Ka ƙarfafa ni, ka cece ni,Gama ina bauta maka, kamar yadda mahaifiyata ta yi.
17Ka nuna mini alherinka, ya Ubangiji,Sa'an nan su waɗanda suke ƙina za su sha kunya,Sa'ad da suka ga ka ta'azantar da ni,Ka kuma taimake ni.