Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
2Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.
3Ya birnin Allah, ka kasa kunne,Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.
4“Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya,Zan sa Masar da Babila a cikinsu,Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha,Su ma na Urushalima ne.”
5A kan Sihiyona kuwa za a ce,“Dukan sauran al'umma nata ne.”Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.
6Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i,Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.
7Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa,Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”