Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
16 verses
1Duk wanda ya je wurin MaɗaukakiZai zauna lafiya,Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,
2Ya iya ce wa Ubangiji,“Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni!Kai ne Allahna, a gare ka nake dogara!”
3Hakika zai kiyaye kaDaga dukan hatsarorin da ka ɓoye,Daga kuma dukan mugayen cuce-cuce.
4Zai rufe ka da fikafikansa,Za ka zauna lafiya a ƙarƙashinsu.Amincinsa zai tsare ka, ya kiyaye ka.
5Ba za ka ji tsoron hatsarori da dare ba,Ko fāɗawar da za a yi maka da rana,
6Ko annobar da take aukowa da dare,Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.
7Mutum dubu za su fāɗi daura da kai,Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai,Amma kai, ba za a cuce ka ba.
8Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.
9Domin ka ɗauka Ubangiji yake kiyaye ka,Maɗaukaki ne yake tsaronka,
10To, ba bala'in da zai same ka,Ba za a yi wa gidanka aikin ƙarfi da yaji ba.
11Allah zai sa mala'ikunsa su lura da kai,Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi.
12Za su ɗauke ka a hannuwansu,Don kada ka buga ƙafarka a dutse.
13Za ka tattake zakoki da macizai,Za ka tattake zakoki masu zafin raiDa macizai masu dafi.
14Allah ya ce, “Zan ceci waɗanda suke ƙaunata,Zan kiyaye waɗanda suka san ni.
15Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu,Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala,Zan cece su in girmama su.
16Zan ba su tsawon rai lada,Hakika kuwa zan cece su.”