Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya,A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,
2A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,Amincinka kuma kowane maraice,
3Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,Da amon garaya mai daɗi.
4Ya Ubangiji,Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,Saboda abin da ka aikataIna raira waƙa domin farin ciki.
5Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!Tunaninka da zurfi suke!
6Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,
7Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
8Gama kai, ya Ubangiji,Maɗaukaki ne har abada.
9Mun sani maƙiyanka za su mutu,Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.
10Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa,Ka sa mini albarka da farin ciki.
11Na ga fāɗuwar maƙiyana,Na ji kukan mugaye.
12Adalai za su yi yabanyaKamar itatuwan giginya,Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.
13Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji,Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.
14Waɗanda suke yin 'ya'ya da tsufansu,A kullum kuwa kore shar suke,Suna da ƙarfinsu kuma.
15Wannan ya nuna Ubangiji adali ne,Shi wanda yake kāre ni,Ba kuskure a gare shi.